IQNA

Kwamitin Kare Hakkin Bil Adama Ya Nuna Rahotonsa Kan Cin Zarafin Rohingya A Myanmar

23:51 - September 10, 2018
Lambar Labari: 3482971
Bangaren kasa da kasa, kwamitin kae hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya nuna rahotonsa dangane da cin zarafin ‘yan kabilar Rohingya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, a yau kwamitin kae hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya nuna rahotonsa dangane da cin zarafin ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Rahoton wanda aka harhada ta har shedu wadanda lamarin ya shafa kai tsaye, da suka hada da wadanda aka kasha iyayensu ko wadanda aka matayensu ko mata da aka sashe mazajensu, ko kuma mutanen da aka azabatr suka samu suka kubuta.

Rahoton ya kara tabbatar da cewa sojojin kasar Myamanr ne suke da alhakin abin da ya faru na kisan kiyashin da aka yi wa musulmin Rohingya a kasar.

3745487

 

 

 

captcha