IQNA

An Buga Wata Makala A Uganda Dangane Da Tarihin Imam Khomeni (RA)

23:54 - June 11, 2019
Lambar Labari: 3483727
Bangaren kasa da kasa, an buga wata makala a kasar Uganda dangane da tarihin rayuwa da kuma gwagwarmayar Imam Khomeni.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na cibiyar yada al’adun musulunci a birnin Kampala na kasar Uganda ta sanar da cewa, ta dauki nauyin buga wata makala da aka rubuta kan tarihin marigayi Imam khomeni wanda ya asassa jamhuriyar musulunci ta Iran.

Bayanin ya ce cibiyar ce ta dauki nauyin buga wannan makala a cikin jaridar Heralad, daga cikin manyan jaridu na kasar Uganda.

Babban abin da makalar tafi mayar da hankali a kansa shi ne, irin gudunmawar da ya bayar wajen fadakar da dukkanin al’ummomin duniya kan makircin manyan kasashe ‘yan mulkin a kan kasashe raunana da masu tasowa.

Makalar ta ce tsayin dakan da ya yi wajen fuskantar manyan kasashen duniya ‘yan mulkin mallaka, ta yi gagarumin tasiri ba kasar Iran ba kawai, har ma da sauran kasashen duniya wadanda ban a musulmi ba, wajen tantance yadda siyasar duniyar yau take tafiya.

3818609

 

 

captcha