IQNA

Martanin Iran Kan Ikirarin Isra’ila Na Shiga Kawance Amurka A Tekun Fasha

23:39 - August 09, 2019
Lambar Labari: 3483928
Bangaren siyasa, Iran za ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar duk wata barazanar tsaro da kawancen Amurka a cikin tekun fasha kan iya haifarwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Sayyid Abbas Musawi  ya ce Iran ta sanar da cewa za ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin fuskantar duk wata barazanar tsaro da kawancen Amurka a cikin tekun fasha kan iya haifarwa bayan da Isra’ila ta sanar da cewa za ta shiga kawance.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Kalubalantar duk wata barazanar Yahudawan Sahayoniyya a yankin tekun Pasha hakkin da ya rataya ne kan kasar Iran.

Kakakin ma’aikatan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Musawi a yau Juma’a ya bayyana cewa: Yiyuwar samuwar sojojin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a yankin tekun Pasha, wata babbar barazana ce ga kasar Iran. Yana mai jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta dauki matakan magance duk wata barazanar Yahudawan Sahayoniyya a yankin.

Abbas Musawi ya kara da cewa: Furucin gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila na yiyuwar shiga cikin rundunar hadin gwiwar Amurka a tekun Pasha, wani makirci ne da ake shiryawa da nufin kunna wutan rikici a yankin na tekun Pasha sakamakon haka hakki ne da ya rataya a wuyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran kare kanta a fagen siyasa da tsaro.

3833641

 

captcha