Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, a yau sojojin Isra’ila sun yi ruwan wuta kan falastinawa a kusa da shingen da yahudawa suka saka a kan iyakan Gaza, inda suka kashe falastinawa hudu.
Sojojin Isra’ila sun kare kansu da cewa wadanann falastinawan suna shirin kai wasu hare-hare ne a kansu, ta hanyar harhada wasu abubuwa da ake zaton bam ne.
Sai dai bayan kashe wadannan fal;astinawa ba a samu komai tare da su ba, illa dai kawai suna tafiya ne a kan hanyar da ke kusa da wurin a lokacin sojojin yahudawan suak kashe su.