IQNA

Madina Birnin Annabi

Madina tana arewacin Riyad a tsakanin Najd, akwai matsanancin zafi a lokacin bazara, da kuma matsanancin sayia lokaci hunturu. Sunan birnin Yasrib kafin zuwan manzon Allah. A cikin birnin akwai masallacin annbi, masallacin Quba da masalalcin Zulqiblatain. Madina na daga cikin birane masu tsarkia wurin musulmi. Kabarin annabi yana kusa da masallacinsa, kuma yana daga cikin wurare masu tsarki na ziyara a wurin musulmi.