IQNA

9:29 - January 03, 2016
Lambar Labari: 3480014
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkin musulmi a Najeriya ta MURIC, ta mayar wa shugaba Buhari da martani, dangane da batun yiwuwar hana saka hijabi a kasar matukar dai aka ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaqna cewa, Kungiyar kare hakkin Musulmi a Nigeria MURIC ta yi watsi da maganar Buhari kan batun yuwuwar gwamnatin kasar na haramta saka hijabi idan ba a samu saukin hare-haren kunar bakin wake ba.
Sanarwa da farfesa akintola ya fitar a madadin kungiyar, ta ce matakin tamkar fakewa da guzuma ne a harbi karsana.
Kungiyar ta fitar da sanarwar ce domin mayar da martani ga kalaman shugaba Muhammadu Buhari a hirarsa da 'yan jarida, na cewar mai yiwuwa gwamnatinsa ta haramta sanya hijabi idan 'yan ta’adda suka ci gaba da yin amfani da mata domin kai hare-haren kunar bakin-wake a arewa maso gabashin kasar.
Hijabi dai ya kasance suturar matan aure da 'yan mata Musulmi masu daman gaske a Najeriya, musamman ma a arewacin kasar.
Sai dai a baya-bayan nan hare-haren kunar bakin-wake da 'yan mata masu sanye da hijabin ke yi sun fara sanya shakku a zukatan mutane dangane da kimar macen da take sanye da irin wannan tufafi.
A lokacin taron kungiyar bunkasa harkokin tatatlin arziki yankin da aka yi a Abuja a makonnin da suka wuce, kungiyar ta yi barazanar haramta saka nikabi domin magance ayyukan 'yan ta'adda.
3471377
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: