IQNA

9:36 - January 03, 2016
1
Lambar Labari: 3480018
Bangaren kasa da kasa, Ayatollah Nimr Baqir Nimr bayan jin cewa an tabbatar da hukuncin kisa a kansa ya aike da wata wasika zuwa ga mahaifiyarsa.
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Alwatan cewa, bayan jin cewa an tabbatar da hukuncin kisa a kansa Ayatollah Nimr Baqir Nimr ya ce; ya mika lamarinsa ga ubangiji.
Bayan jin cewa an tabbatar da hukuncin kisa a kansa sai ya aike da  wasika zuwa ga mahaifiyarsa da ke cewa:
Zuwa ga mahaifiyata Ummu Ja'afar;
Mahaifiyata ina godiya ga Allah kan duk abin da ya kaddara mani, Allah shi ne yafi sani a kan komai da ya shafi da kuma karshen lamarinmu, duk abin da Allah ya zama a kanmu shi ne mafificin zabi da kuma mafi alkhairi gare mu, muna yin zabi, amma Allah yana zabar mana abin da ya fi a gare mu.
A lokacin da ya zama Allah shi ne mai jibintar lamarina kuma yake sane da halina, wannan shi kadai ya ishe ni, Allah shi ne mahaliccinmu baki daya, kuma shi ne ya tsara tare da kaddara komai da ya shafi rayuwarsu.
Babu wani wanda ya isa ya aikata wani abu a cikin duniyar nan face da sanin Allah, babu wani abu da ke wajen sanin Allah da ikonsa, mahaifiyata ina rokon Allah yak are ki ya kuma kare dukkanin bayinsa.
3472915
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 4
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Ba A San Shi Ba
0
1
tanx
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: