IQNA

15:45 - January 04, 2016
Lambar Labari: 3480023
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci ya bayyana cewa, babu makawa daukar fansa irin ta ubangiji tanan nan tafe kan masarautar Al Saud kan kisan da suka yi wa Sheikh Nimr.

Kamfanin dillanicn labaran iqn aya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na jagora cewa, A safiyar yau Lahadi ne, a wajen darasin Bahasul Kharij da yake bayarwa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei yayi kakkausar suka ga zartar da hukuncin kisa a kan babban malamin nan mumini Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Saudiyya ta yi a jiya inda ya kirayi duniya baki daya da ta sauke nauyin da ke wuyanta dangane da wannan danyen aikin da kuma wasu makamantan hakan da gwamnatin Saudiyya take aikatawa a kasashen Yemen da Bahrain. Jagoran ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu nan ba da jimawa ba za a ga tasirin jinin wannan shahidi da aka zalunta da aka zubar ba bisa hakki ba. Lalle Allah zai dau fansa a kan shugabannin Saudiyya.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Wannan malamin da aka zalunta, bai kasance yana kiran mutane da su dau makami ba, kamar yadda kuma ba a boye yake ayyukansa ba, face dai abin da yake yi shi ne sukan (gwamnati) a fili da umurni da kyakkyawa da hani da mummuna da ya ginu bisa koyarwa ta addini.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana shahadar Sheikh Nimr da kuma zubar da jininsa da aka yi ba tare da hakki ba a matsayin babban kuskure na siyasa da gwamnatin Saudiyya ta aikata yana mai cewa: Allah Madaukakin Sarki ba zai rufe ido dangane da jinin wanda bai ci bai sha ba da aka zubar. (Ko shakka babu) jinin da aka zubar ba bisa hakki ba zai hau kan shugabannin wannan gwamnati (ta Saudiyya).

Har ila yau kuma yayin da yake kakkausar suka ga shirun da masu ikirarin ‘yanci, demokradiyya da hakkokin bil'adama suka yi da kuma goyon bayan da suke ba wa gwamnatin Saudiyya wace ta ke zubar da jinin wanda bai ci bai sha ba babban laifinsa kawai shi ne suka da nuna rashin amincewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: wajibi ne duniyar musulmi da kuma dukkanin duniya su sauke nauyin da ke wuyansu dangane da wannan lamarin.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cutarwa da azabtar da al'ummar Bahrain da sojojin Saudiyya suke yi haka nan da rusa masallatai da gidajensu da kuma sama da watanni 10 na ruwan bama-bamai da suke yi a kan al'ummar kasar Yemen a matsayin wasu daga cikin misalan danyen aikin gwamnatin Saudiyya, daga nan sai ya ce: Wajibi ne mutanen da suka damu da makomar bil'adama da kuma hakkokin bil'adama damuwa ta gaskiya da hakika, wajibi ne su ci gaba da bibiyen wadannan lamurran. Bai kamata su ci gaba da rufe ido kan su ba.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kara da cewa: Ko shakka babu Shahid Sheik Nimr zai kasance cikin falala da rahamar Ubangiji, sannan kuma ko shakka babu fansa ta Ubangiji za ta hau kan azzaluman da suka kashe shi da kuma wuce gona da iri kan rayuwarsa. Hakan kuwa shi ne abin da ke kwantar mana da hankali.

3463996


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: