IQNA

Wahabiyanci Shi Ne Matsalar Duniya A Yau

16:49 - January 18, 2016
Lambar Labari: 3480053
Bangaren kasa da kasa, Isma’ila Muraimi shugaban cbiyar yada aladun muslunci ta Marcelle a kasar Faransa a lokacin ganawa da shugaban karamin ofishin jakadancin Iran ya bbayyana wajabci karfafa hadan kan musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga bangaren yada labarai na ciyar yada ala’dun muslunci cewa, Sayyid Abdulamir Musavi Badr shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Algeriya ya gana da Isma’il Muraim shugaban cibiyar yada al’adun muslunci ta Marcelle a kasar Faransa, a karamin ofishin jakadancin kasar Iran da ke kasar Algeria.

Shugaban cibiyar ta al’adun muslunci a Marcelle ya bayyan acewa akwai bukatar samar da taimako na musaman daga Iran ga musulmin wannan yanki, ta fuskar koyarwa da kua yada addini.

Muraimi dan asalin kasar Algeriya ne, amma yana rayuwa akasar faransa, kuma yana kira zuwa ga hadin kan al’ummar musulmi tare da ajiye duk wani abin da ka iya kawo sabani a tsakanin muslumi, da kuma fuskantar masu kokarin yin hakan, musamman wahabiya da takfiriyawa.

A cikin watan gobi mai kamawa ne Muraimi tare da wata tawaga daga cibiyar yada ala’dun muslunci ta Marcelle za su kawo wata ziyarar bude a Tehran, inda za su gana da wasu daga cikin jami’a a wannan bangare.

3468377

captcha