IQNA

23:51 - February 11, 2016
Lambar Labari: 3480129
Bangaren kasa da kasa, shugaban kwamitin kula da harkokin kur’ania ma’aikatar kula da addini a Syria ya ce za a girmama masu koyon karatun kur’ani mai tsarki a masallatan birnin Damascus.

Muhammad Anas Al-dawaminah shugaban kwamitin kula da harkokin kur’ania ma’aikatar kula da addini a Syria a zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayyana cewa, za a girmama masu koyon karatun kur’ani mai tsarki a masallatan birnin Damascus a bangarorin harda da kuma karatu.

Ya ce za a gudanar da zaman girmama wadanda suka nuna kwazon ne a masallatan yankunan Bu’aira, Anis, da kuma Dakkul bab da ke a cikin gundumar Damscus.

Muhammad Anas Al-dawaminah ya Klara da cewa makarantar Imam Gazali ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan taro na girmama daliban a bangaren karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki.

Muhammad Anas Al-dawaminah mahardacin kur’ani mai tsarki ne, wanda kuma shi ne ke jagorantar kwamitin kula da harkokin kur’ani a ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar.

3474717

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: