IQNA

A Yau Za A Gudanar:
21:53 - May 29, 2016
Lambar Labari: 3480458
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a gudanar da zagayen karshe na gasar kur’ani ta tartili da kyawun sauti a babban masallacin cibiyar Azhar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Bawaba News cewa, ana gudanar da wannan gasa ne ta hadin gwiwa tsakanin cibiyar Azhar da kuma hukumar radio ta kasar Masar.

Mataki na farko gasar tana faraway ne da masu gasa fiye da dubu daya daga dukkanin lardunan kasar Masar, sai kuma kimanin mutane 500 daga cikin yan kasashen ketare mazauna kasar.

Daga cikin dukkanin masu halartar gasar ne ake zabar wadanda za su kai ga mataki na karshe, wadanda su kuma daga cikinsu za a zabi mutane 10 wadanda suka fi kowa iya karatu da kyawun sauti da ake bukata.

A yau ne dai za a gudanar da mataki na karshe na wannan gasa, inda za a sam halartar jami’ai na hukumar radio Masar da kuma wasu fitattun alkalai a bangaren gasar kur’ani, da suka hada da Sheikh Ahmad Ahmad Nu’ainua da kuma sheikh Abdullafattah Taruti sai kuma sheikh Mahmud Alkhesht.

Mutane goma da za a zaba su ne za su zama masu karatun kr’ani mai tsarki a gidan radio Masar a cikin wannan watan azumin ramadsana mai alfarma, kuma za a bas u kyautuka na musamman daga wannan hukuma.

3501898

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: