IQNA

An Yi Allawadai Da Keta Alfarmar Masallaci A Firka Ta Kudu

23:51 - January 17, 2017
Lambar Labari: 3481144
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kare hakkokin musulmi a kasar Afirka ta kudu ta yi Allawadai da keta alfarmar wani masallacia garin Cape ta yamma.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwafd cewa, kungiyar kare hakkokin usulmi na Afirka ta bayyana aikin da wasu bata gari suka yin a keta alfarmar masallacin da aka gina shekaru fiye da 100 da cewa aiki ne na dabbanci.

A cikin bayanin da kungiyar ta fitar ta bayayna cewa wasu mutane da ba a san ko su wane n ba suka jefa naman alade da kazantarsa cikin masallaci, wanda musulmi suke yin salla a cikinsa.

Bayanin y ace haki wannan aiki ne na tsokana, amma musulmi ba asu dauki mataki na rashin bin doka da kaida ba, a kan kungiyar tace tana kira ga gwamnati da ta dauki matakan da suka dace domin gano wadanda suke da ahnnua cikin lamarin.

Kasar Afirka ta kudu na daga cikin kasashen da smuulmi suke zaman lafiya da al'ummar kasar, amma a cikin 'yan shekarun baya-bayan nana, ana samun bullar kungiyoyi na masu tsatsauran ra'ayin kyamar musulunci.

Daga cikin ayyukan da suke yi kuwa har da keta alfarmar masallatai kamar yadda aka yi a wannan masallaci da ke birnin Cape ta yamma, wanda kuma hakan yake nuni da cewa lamarin yana daukar wani sabon salon a tsananta.

3563656

http://iqna.ir/fa/news/3563656

captcha