IQNA

An Sake Bude Cibiyar Adana Kayan Tarihi A Birnin Alkahira

23:24 - January 18, 2017
Lambar Labari: 3481147
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Masar a yau 18/1/2017 ya sake bude cibiyar adana kayan tarihi ta birnin Alkahira.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Alnahar cewa, a yau Abdulfattah Sisi shugaban kasar Masar ya sake bude cibiyar adana kayan tarihi da ke birnin Alkahira.

Tun daga shekara ta 2014 da aka kai wani harin bam a birnin Alkahira, aka rufe wannan babbar cibiyar kayan tarihin muslunci, wadda tana daya daga cikin wuraren adana kayan tarihi mafi muhimmanci a duniya, sakamakon lalacewar wani bangaren ginin cibiyar.

Wannan cibiya na daga cikin cibiyoyin da masu bincike daga dukkanin kasashen duniya suke suke gudanar da ayyukansu a cikinta, baya ga kayan tarihin muslunci, akwai wasu abubuwa na daban da tarihinsu ke koma zuwa ga dubban shekaru da suka gaba.

Yanzu haka dai an iya gyara kayayyki 160 daga cikin kayan tarihi 179 da suka lalace sakamakon harin da aka kai a kan hedikwatar tsaro da ke kusa da cibiyar.

Daga cikin kasashen da suka dauki nauyin aikin gyaran wannan cibiya akwai Amurka, UAE, Switzerland, Italia da kuma UNESCO.

3564282

captcha