IQNA

Kasashen Musulmi Za Su Ci Gaba Da Matsa Lamba A Kan Myanmar

23:54 - January 19, 2017
Lambar Labari: 3481148
Bangaren kasa da kasa, a zaman da jami'an kasashen musulmi suka gudanar yau a Malaysia sun cimma matsaya kan matsa lamba akan Myanmar.

BKamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin «Middle East Eye» cewa, a yau jami'an kasashen musulmi ammbobia kungiyar OIC sun gudanar da zama a kasar Malaysia, inda suka tattauna dangane da halin da musulmi suke cikia kasar Myanmar.

Tun daga cikin watan Oktoban da ya gabata ne dai bayan kisan wasu jami'an 'yan sanda 9 a wani yanki na 'yan kabilar Rohingya, jami'an tsaron kasar tare da umarnin mahukuntan kasa suka shiga yin kisan kiyashi a kan msuulmi.

Sakamakon daukar irin wadannan tsauraran matakai na murkushewa a kan msuulmi, dubbai daga cikinsu sun tsere sun bar muhallansu, kamar yadda kuma aka kone gidaje da dama mallakinsu, wanda hakan ya sanya su yin gudun hijira a cikin kasar da ma wasu kasashen yankin.

Jami'an diplomasiyya na kasashe 57 mambobi a kungiyar hadin kan kasashen msuumi suka halarci taron na yau.

3564359


captcha