IQNA

Kamfe Mai Taken "Kur'ani Littafin Da Ya Girgiza Duniya" A Australia

23:57 - January 19, 2017
Lambar Labari: 3481149
Bangaren kasa da kasa, an kaddamar da wani kamfe a kasar Australia mai taken kur'ani littafin da ya girgiza duniya wanda musulmin kasar suka kaddamar.

BKamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na «ireaworld» cewa, a daidai lokacin da kyamar muslunci da yada maganganu na karya a kan kur'ani ke ci gaba da kara yaduwa, ya zama wajibi a samar da wani shiri an kalubalantar hakan a ilmance.

Wasu daga cikin masana musulmi a babbar kwalejin nazari da bincike kan msuulunci ne suka kaddamar da wanannkamfe, da nufin kara wayar da kan al'ummar kasar ta Australia a kan kur'ani mai tsarki da kuma koyarwarsa, wadda ita ce hakikanin koyarwar addinin muslunci.

A cikin wani bayani da suka fitar sun bayyana cewa, akwai hanyoyi da dama da za a yi amfani da su a cikin wannan kamfe, da hakan ya hada da rubutu da kuma shirya taruka domin gabatar da jawabai da kuma amsa tambayoyi daga mutane daban-daban kana bin da ya shige msuu duhu dangane da muslunci da kuma kur'ani.

Haka nan kuma za a rika shirya tarukan baje koli domin nuna wasu daga cikin abubuwa da suka shafi kur'ani, kamar fitar da ayoyi da suke kira zuwa zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin al'ummomi, wanda kur'ani yak eyin kira a kai.

Kamar yadad za a bayar da kwafin kur'ani kyauta ga mutane wanda aka tarjama a cikin harshen turanci domin su karanta suga abin da ke ciki.

3564360


captcha