IQNA

Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Kan Wasu Masu Fafutuka 4 A Bahrain

23:58 - January 19, 2017
Lambar Labari: 3481150
Bangaren kasa da kasa, kotun masarautar Bahrain ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan mutane hudu bisa zarginsu da kisan kai.
Hukuncin Daurin Rai Da Rai A Kan Wasu Masu Fafutuka 4 A Bahrain

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar alalam cewa, shafin Lu'lu'u ya habarta cewa, daga cikin mutanen hudu biyu daga cikin kuma an daure su shekaru goma a gidan kaso kari bisa daurin da ke aknsu.

Mahukuntan masarautar ta Bahrain ta kame dukkanin mutanen ne guda hudu da ma wasu an daban, wadanda suke adawa da salon tsarin mulkin kasar na mulkin mulukiya da kama karya, wadanda suke neman sauyi ta hanyar lumana.

Baya ga wadannan mutane hudu, masarautar ta daure wasu mutane 8 a gidan kaso a tsakanin shekaru 3 zuwa 6 kowannensu.

Wadannan hukunce-hukunce na kotun masarautar kasar ta Bahrain dai suna zuwa ne bayan kisan da aka yi wa wasu matasa uku masu fafutuka ta siyasa ta hanyar lumana, wadanda aka kasha sub a tare da bayyana wa duniya wani dalili mai gamsarwa kan kisan da aka yi msuu ba.

Yanzu haka dai al'ummar Bahrain suna ci gaba da gudanar da gangami da jerin gwano domin nuan rashin amincewarsu da wannan kisan kai da masarautar kasar ta yi kan 'yan kasa saboda dalilai na siyasa da kuma nuna banbancin mazhaba.


3564428


captcha