IQNA

ISESCO Za Ta Halarci Taron Sanar Da Mashhad A Matsayin Birnin Al’adun Muslunci Na 2017

22:46 - January 20, 2017
Lambar Labari: 3481153
Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada al’adun mulsunci ta kasashen musulmi ISESCO ta sanar da cewa mataimakiyar babban sakataren kungiyar za ta halarci taron sanar da Mashhad a matsayin birnin al’adun muslunci na 2017.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ISESCO cewa, Amina Alhujri mataimakiyar babban sakataren kungiyar Abdulaziz Usman Al-tuwaijari za ta halarci taron bayyana Mashhad a matsayin birnin tarihi da al’adu na muslunci na shekarar 2017, tare da karan jawabin babban sakataren.

Bisa ga sanarwar da shafin an ISESCO ya bayar, a ranar Talata mai zuwa ne za a gudanar da wannan taro a birnin na Mashhad, wanda kuma zai samu halartar wasu daga cikin jami’ai na yankin, da kuma ministan al’adu na kasar Iran.

A ranar Litinin dai ake sa ran mataimakiyar babban sakataren kungiyar ta ISESCO ta iso birnin na Mashhad na kasar Iran, inda za ta gana da jami’an kasar, kafin ranar Talata kuma ta jagoranci kaddamar da mika wannan matsayi ga mahukunta na kasar ta Iran.

Kungiyar ta ISESCO dai ta bayar da wannan matsayi ga birane 4 na kasashe daban-daban, da suka hada da birnin na Mashhad, Snar na Sudan, Amman na kasar Jordan, sai kuma Kampala na kasar Uganda, a matsayin birane hudu na al’adun muslunci na shekarar 2017.

3564551

captcha