Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, dukkanin al'ummar palastinu suna adawa da wannan shiri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke neman a hana palastinawa yin kiran salla a cikin yankunansu.
Ahmad Mudallil daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadul Islami ya bayyana cewa, wannan mataki yana daidai da sauran ayyukan ta'addanci na Isra'ila, kuma yana a matsayin ci gaba da take hakkokin Palastinawa da cin zarafinsu da kuma keta alfarmar addininsu da Isra'ila ke yi a tsawon tarihinta.
Ahmad Abu Haliba shugaban cibiyar Al-quds ya bayyana cewa, a'ummar Palastinu ba ta taba amincewa da wannan sabuwar doka ta zalunci da Isra'ila ke neman kafawa a kansu ba, domin kuwa kiran salla wani bangare na addini, da ba za a raba al'ummar musulmi na palastinu da shi ba.
Tun a cikin shekarar da ta gabata ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara batun hana Palastinawa yin kiran sallah, amma batun ya fuskanci tsaiko daga majalisa, inda a halin yanzu gwamnatin Netanyahu ta sake shirya wani sabon daftarin kudiri a kan wannan batu.