IQNA

Bankin Musulunci Zai Yi Aiki Tare Da Cibiyoyin Agaji A Birtaniya

21:52 - February 20, 2017
Lambar Labari: 3481249
Bangaren kasa da kasa, bankin muslunci nan a Alrayyan na kasar Birtaniya ya bayyana cewa zai yi aiki tare cibiyoyin da ke gudanar da ayyukan alkhari da ke London da wasu biranan kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin «fundraising» cewa, bankin musluncin zai ya bayyana cewa zai yi aiki tare da irin wadannan cibiyoyi ne domin karfafa ayyukansu da suke gudanarwa na taimakon marassa karfi.

Daga cikin ayyukan da cibiyoyin ke gudanarwa wadanda za su aiki tare da wannan banki har da samar da kayyakin bukatar rayuwa ga masu fama da matsaloli a wasu kasashe, da hakan ya hada da kasar Mali da ma wasu kasashen Afirka.

Haka nan kuma daga cikin kayan da za su samar har da abinci tufafi da ma wasu abubuwan na daban domin taimaka ma mutane, kamar yadda kuma bankin zai karbi hannayen jari daga masu bukatar taimaka wadannan kungiyoyi, domin karfafa ayyukan jin kai.

Baya ga wannan akwai ayyuka na kawasunci wadanda bankin yake gudanarwa, wadanda za su taimaka ma masu karamin karfi da suke bukatar saka hannayen jari domin samun amfani bisa kaidoji na muslunci.

3576507


captcha