IQNA

An Kammala Aikin Gyaran Kwafin Kur’anin Sayyid Nafisah A Masar

23:52 - February 21, 2017
Lambar Labari: 3481252
Bangaren kasa da kasa, cibiyar kula da littafai na tarihia kasar Masar ta sanar da kammala aikin gyaran kwafin kur’anin Sayyidah Nafisah.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Al-dastur cewa, Muhammad Al-daba shugaban cibiyar adanalittafan tarihi a Masar bayyana cewa, bangaren gyaran tsoffin littafai na wannan cibiya ya kammala aikin gyaran kwafin kur’anin Sayyid Nafisah.

Ya ci gaba da cewa, yanzu haka ana gudanar da bincike kan tarihin wannan kur’ani wanda masallacin sayyid nafisa ya bayar da shi kyauta ga wannan cibiya a cikin shekara ta 1878.

Sayyid Nafisah dai tana daga cikin jikokin Imam Hassan Mujtaba (AS) dan Fatima diyar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa tsarkaka, kuma ta auri dan Imam Jafar Sadiq (AS) ta rasua cikin shekara ta 208, inda kabarinta yake a kasar Masar.

Hubbarenta na daga cikin hubbarorin da aka gina akasar ta Masar tun lokacin mulkin dalaur Fatimiyyah, inda yanzu ake ziyartar wannan wuri mai albarka daga wurare daban-daban na kasashen musulmi.

3576697


captcha