IQNA

Wilders Ya Sha Martani Daga Cibiyar Fatawa A Masar

20:39 - March 09, 2017
Lambar Labari: 3481299
Bangaren kasa da kasa, Cibiyar da ke bayar da fatawoyin muslunci a kasar Masar ta mayar da kakkausan martani a kan kalaman batunci da dan majalisar dokokin Holland Geert Wilders ya yi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Almisriyun ya bayar da rahoton cewa, cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da kalaman da suka fito daga bakin dan majalisar dokokin kasar Holland Geert Wilders, da ke danganta muslunci da ta'addanci, da kuma yin kira da a rufe dukkanin masallatai a kasar, tare da kwace duk wani kwafin kur'ani mai tsarki da aka samu a hannun wani.

Wlders wanda fitacce ne wajen nuna tsananin gaba da kyama ga addinin muslunci da kuma musulmi, ya bayyana hakan ne a wata zantawa da ta hada da tashar talabijin ta Euronews, inda ya ce idan ba adauki matakan gaggawa wajen taka wa musulmi birki ba, za su mayar da nahiyar turai wani babbar tunga ta 'yan ta'adda.

A kan ya ce yana kira ga mahukunta akasar Hollanda da ma sauran kasashen turai, da su rufe duk wani masallaci ko wata cibiya ta muslunci, tare da hana musulmi shiga cikin kasashensu, kuma su kore dukkanin msuulmin da suke kasashensu, domin a cewarsa ta haka ne kawai kasashen turai za su zauna lafiya.

Babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar Masar ta bayyana wannan furuci da cewa, furuci ne mai matukar hadari, wanda ya kamata mahukunta a kasashen turai su dauki matakia kansa, domin kuwa zai kara jefa rayukan musulmi da suke zaune a kasashen turai a cikin hadari.

3581916

captcha