IQNA

Mahukunta A Jahar Michigan A Amurka Sun Yi Allawadai Da Kone Masallaci

23:39 - March 14, 2017
Lambar Labari: 3481313
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a jahar Michigan ta kasar Amurka sun yi Allawadai da kakkausar murya kan kone wani masallaci mallakin musulmi da aka yi a cikin jahar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin mlive cewa, jami’an tsaro sun shiga gudanar da bincike kan kone masallacin musulmi da aka yi a garin Pittsfield na jahar Michigan a kasar Amurka.

Ofishin magajin garin birnin ya fitar da bayani na yin Allawadai da kakakusar murya kan wanann aiki na rashin lissafi, tare da bayyana cewa musulmi da suke cikin birnin duk daya suke da sauran al’umma, suna hakkokinsu kamar yadda kowa dan kasa yake da hakki.

Bayanin ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike domin tattabatar da cewaan gano dukkanin wadanda suke da hannua cikin wannan ta’asa domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Shi ma a nasa bangaren Debby Dingal dan majalisar dokokin Amurka daga jahar ta Michigan ya bayyana cewa, ya yi bakin ciki matuka a lokacin da ya ji labarin cewa wasu mutane sun kone masallacin musulmi a jahar da yake wakilta a majalisar dokokin Amurka.

Ya ce abin takaici yadda yadda ake samun karuwar kyamar musulmi a wasu daga cikin jahohin Amurka, amma jaharsa ba za a taba lamunce faruwar irin wanann aiki na dabbanci ba.

3584078

captcha