IQNA

An Gudanar Da Maulidin sayyidah Zahra (SA) A Saudiyya

22:47 - March 19, 2017
Lambar Labari: 3481326
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da maulidin shugabar matan duniya da na lahira Sayyida Fatima Zahra (SA) a yankin Qatif na kasar saudiyyah.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Juhainah News cewa, Mabiya mazhabar Ahlul bait (AS) 'yan kasar Saudiyyah, sun gudanar da tarukan Maulidin Sayyidah Fatimah Zahra (amincin Allah ya tabbata a gare ta) a gundumar Qatif da ke gabashin kasar ta Saudiyyah a daren jiya Asabar.

A wurin taron dai an gabatar da jawabai ga mahalarta, dangane da matsayin wannan baiwar Allah wadda Allah madaukakin sarki ya sanya ta ta zama mafi soyuwar dukkanin talikai a wurin manzon Allah, kamar yadda kuma ya fifita a kan dukkanin mata na duniya da lahira.

An gudanar da wannan taro a wurare daban-daban na yankunan gabashin Saudiyya, wadanda yankuna ne na mabiya mazhabar ahlul bait ko kuma 'yan shi'ar ahlul bait (AS).

Daga cikin abubuwan da aka gudanar har da wakoki na yabonta da kuma mahaifinta tsira da amincin Allah su tababta a gare shi da iyalan gidansa tsrkaka, da kuma mijinta da 'ya'yanta tsarkaka.

3585269
captcha