IQNA

Khatmar Kur'ani Mai Tsarki A Kasar Jordan

22:43 - March 21, 2017
Lambar Labari: 3481334
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani shiri na safkar kur'ani mai tsarki a kasar Jordan a cikin watan azumi mai zuwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wannan shiri zai gudana nea karkashin ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar Jordan a dukkanin masallatan kasar.

Minista mia kula da harkokin addini na kasar ya bayyana cewa, za a gudanar da wani shiri ne a cikin azumi mai zuwa a masallatai da daman a kasar, kuma yanzu haka an gana da limamai da daman a masallataia garuruwa daban-daban kan yadda za a gudanar da shirin.

Shirin dai dai zai kasance na karatun kur'ani ne, kuma kowane masallaci akwai adadin safkar da zai daga farkon watan Ramadan zuwa karshe, inda daga karshe bisa issafin da aka za a yi safkar kur'ani dubu sittin.

3585377
captcha