IQNA

Kasashe 40 Ne Za Su Halarci Gasar Kur’ani

23:44 - March 22, 2017
Lambar Labari: 3481336
Bangaren kasa da kasa, ya zuwa yanzu haka kimanin kasashe 40 ne suka sanar da cewa a shiye suke halarci gasr kur’ani mai tsarki karo 24 Ta Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Masar ta sanar da cewa, kasashen duniya 40 ne suka bayyana shirin na halartar gasar kasa da kasa da za a gudanar a kasar.

Bayanin ya ce ministan ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Masar Mukhtar Ali Juma’a shi ne zai jagoranci bude wannan gasa da za a gudanar nan da ‘yan makoni masu zuwa a birnin Alkahira fadar mulkin kasar ta Masar.

Baya ga ministan kula da harkokin adini na Masar, wasu daga cikin jam’an gwamnatin kasar da ma wasu jami’ai daga kasashen muuslmi za su halarci taron bude gasar.

Babbar manufar gudanar da wannan gasa dai ita ce samar da yanayi na karfafa gwiwar matasa domin mayar da hankali kan kur’ani mai tsarki, ta fuskar karatu da harda da kuma koyon ilmominsa.

3585443


captcha