IQNA

'Yar Wasa Mai Hijabi A Amurka Ta Aikewa Trump da Budaddiyar wasika

21:21 - March 23, 2017
Lambar Labari: 3481340
Banagren kasa da kasa, Ibtihaj Muhammad 'yar wasan suka da takobi da ta samo wa kasar Amurka lambar yaboa wasannin motsa jiki ta aike da budaddiyar wasika zuwa ga Trump.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin «aboutislam» cewa, Ibtihaj ta aike da wasikar tata, wadda ta kunshi korafi ga shugaban kasar Amurka Donald Trump kan salon siyasarsa ta kin jinin musulmi.

A cikin wasikar Ibtihaj Muhammad ta ce, shugaba Trump sakamakon salon da ka yi amfani da shi a cikin yakin neman zabenka na nuna kin jinin musulmi da masu yin hijira zuwa Amurka, hakan ya haifar da mummunar matsala ga wani bangare na al'ummar Amurka saboda addininsu.

Ta ce ni 'yar kasar Amurka ce amma kuma musulma, kuma duk da haka ina wakilci Amurka a hukumance a wasanni motsa jiki na duniya har ma na samo lambar yabo ga kasar Amurka, amma na a filin safkar jirgin sama an hana wucewa, an yi bincike a kaina tamkar mai laifi, kuma an bude wani file na musamman domin bincike ke a kaina, duk wannan ya zo bayan da ka dare kan shugabancin kasar Amurka.

Babban kure ne a danganta ta'attanci da duk wani musulmi ko wani wanda ya hijira daga kasarsa zuwa Amurka, yin hakan ba adalci ba ne, kuma ya sabawa abin Amurka ta ginu a kansa, saboda haka ina kira gare k aka sake salon siyasarka ta kin jinin musulmi.

Ibtihaj Muhammad ta sami kyautar tagulla a gasar motsa jiki ta duniya da aka gudanara birnin Rio na kasar Brazila shekarar da ta gabata kuma tana sanye da hijabinta na muslunci.

3585486
captcha