IQNA

Azhar Ta Yi Allawadai Da Harin Da Aka Kai Yau A Masar

23:28 - April 09, 2017
Lambar Labari: 3481390
Bangaren kasa da kasa, bababr cibiyar musulunci ta kasar Masar ta yi Allawadai da kakakusar murya dangane da harin da aka kai yau a kan majami’ar mabiya addinin kirista.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, akalla mutane talatin ne majiyoyin gwamnatin kasar Masar suka tabbatar da mutuwarsu a wani harin bam da aka kai yau a cikin garin Tanta da ke arewacin birnin Alkahira na kasar Masar.

An tayar da bam din ne a kusa da babbar majami'ar mabiya addinin kirista da garin Tanta, mutane 15 sun rasa rayukansu a nan take, yayin da mutane kimanin 40 kuma suka samu raunuka.

Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da mabiya addinin kirista suke shirin tarbar babban jagoran kiristoci mabiya darikar katolika paparoma Francis a kasar ta Masar nan da kwanaki goma masu zuwa.

Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin dai yana ci gaba da karuwa, inda a yanzu ake maganar cewa adadin yah aura mutane talatin.

Hare-haren bama-bamai sun kara ta’azzara ne a kasar masar a cikin kwanakin baya-bayan nan, musamman tun bayahn da Masar ta shiga takun saka da saudiyya, inda Masar ta ce bata goyon bayan rikicin da larabawa suka haddasa a Syria.

3588254


captcha