Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Al-shuruq ta kasar Masar ta bayar da rahoton cewa, Fadi Francis daya daga cikin mambobin kwamitin tsara tafiye-tafiyen Paparoma a fadar Vatican ya sheda cewa, tafiyar Paparoma zuwa Masar na nan kamar yadda aka tsara.
Fadi Francis ya ce babu gaskiya a cikin rahotannin da wasu kafofin yada labarai suka yada, da ke cewa Paparoma ya dakatar da tafiyarsa zuwa kasar Masar, sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kai a kan manyan majami’iun mabiya addinin kirista a kasar.
A ranar 27 ga wannan wata na Afrilu ne dai paparoma Francis zai kai ziyara ta kwanaki biyu a kasar Masar, inda zai gana da shugaban kasar Abdulfattah Sisi, da kuma babban jagoran mabiya addinin kirista na kasar, gami da babban malamin cibiyar Azhar.