IQNA

Isra'ila Ta Bayar Da Umarnin Rusa Wani Masallaci A Gabashin Birnin Quds

20:29 - April 14, 2017
Lambar Labari: 3481406
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayar da umarnin rusa wani masallaci a gabashin birnin Quds, bisa hujjar cewa ba a gina shi bisa ka'ida ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar pressTV ta bayar da rahoton cewa, haramtacciyar kasar Isra'ila ta bayar da umarnin rusa masallacin Abdullah Al-sinawi da ke yankin Salwan a gabashin Quds.

Wannan masallaci na daya daga cikin masallatai shida da haramtacciyar kasar Isra'ila ke shirin rusawa a yankin, bisa hujjar cewa an gina su ne ba bisa ka'ida ba.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta OCHA ta bayar da wani rahoto da ke cewa, a duk lokacin da Isra'ila take son gina matsugunnan yahudawa a cikin wani na Palastinawa, tana fakewa da cewa an gina gidaje a yankin ba bisa ka'ida, inda ta kan rushe gidajen Palastinawa da masallatai da makarantunsu, daga bisa kuma ta gina matsunnan yahudawa a wuraren.

Bayanin kungiyar ya ce babu wani dalili na rusa masallatan palastinawa a yankin Salwan, hakan yana da alaka ne kawai da shirin Isra'ila na gina wasu sabbin matsugunnan yahudawa a cikin yankin mallakin Palastinawa, inda ake rusa musu gidaje da kaddarori ba tare da biyansu diyya ba.

3589435

captcha