IQNA

Kare Hakkin Bil Adama A Cikin Kur’ani A Taron Tunisia

23:35 - April 15, 2017
Lambar Labari: 3481410
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanr da wani taro karkashin kungiyar NHRC wanda ya shafi kare hakkin bil adama a mahangar kur’ani mai tsarki da addinin muslunci a kasar Tunisia.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa,a yau an bude wani taro wanda ya hada da baje kolin kur’ani a birnin Tunis na  Tunisia mai taken kare hakkokin bil adama mahangar kur’ani mai tsarki.

Wannan taro wanda wannan kungiya ta kasar Qatar ta dauki nauyin shiryawa, ya samu halartar Abdullahi bin Nasir Al thani firayi ministan kasar Qatar, tare da wasu daga cikin ministocin kasar da kuma jami’ai.

Bisa ga bayanin kungiyar, wannan taro na da nufin isar da sakon kur’ani ne a bangaren kare hakkokin bil adama, ta hanyar gabatar da jawabai na malamai, da kuma baje kolin ayoyi masu magana a kan wannan bangare.

Wannan dai bas hi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan taro ba, wanda kan fitar da bayanai a kan yadda ake sukar muslunci da danne hakkokin bil adama, sabanin abin da yake a cikin wannan addini mai girma

Kur’ani mai tsarki shi ne littafin da yake a kan gaba wajen kare mutuncin dan adam da hakkokinsa, domin kuwa hukunce-hukunce da suka shafi hakkoki su ne suka tsauri a cikin kur’ani, wadanda muslunci baya yin saku-saku da su.

Manzon Allah (SAW) wanda shi ne ya zo da wannan addini mai girma, shi ne wanda ya koyar da duniya yadda ake kare hakkokin bil adama da girmama shi da kare mutuncinsa.

3589574



captcha