IQNA

Senegal Za Ta Fara Amfani Da Tsarin Kudi Na Muslunci

23:47 - April 16, 2017
Lambar Labari: 3481411
Bangaren kasa da kasa, an kaddamar da tsarin bankin muslunci da kuma saka hannyen jari bisa tsarin muslunci a kasar Senegal.

BKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ina cewa, wannan sabon tsari zai fara iki daga cikin wannan mako

Tasrin dai zai shafi bangaren saka hannayen jari da kuma saka kudaden ajiya ba tare da karin kudin ruwa ba, kamar yadda kuma za a iya gudanar da sauran mu'maloli na kudia karakshin wananntsari daidai da shari'a ta muslunci.

Kasar Senegal ta kaddamar da wannan tsari a hukumance, tare da halartar manyan jami'ai a bangaren harkar kudade da bankuna na kasar, ta yadda tsarin ya amaa daidai da sauran tsare-tsare na bankuna, da kuma cibiyoyin saka hannayen jari na kasar.

Bankin muslunci na samun karbuwa a kasashen Afirka da kuma na Asia, sakamakon yadda ake gudanar da mu'amala bisa tsarin muslunci, wanda ya sha banban da sauran tsare-tsare na harkokin kudi na bankuna a duniya.

Yanzu haka dai mutane da dama a kasar ta Senegal sun nuna farin cikinsu da kuma karbar wannan tsari a matsayin muhimmin lamaria gare su, wanda za su amfana da shi a bangarori daban-daban na harkokin tattalin arzikinsu.

3590125
captcha