IQNA

An Bayar Da Kyatar Kur’ani Ga Makarantan Kur’ani A Ghana

23:50 - April 19, 2017
Lambar Labari: 3481419
Bangaren kasa da kasa, an bayar da kyautar kwafin kur’ani mai tsarki makaranta kur’ani da za su wakilci kasar Ghana a gasar kur’ani ta kasa da kasa da za a gudanar a Iran.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin makaranta kr’ani mai tsarki da suka samu nasarar lashe gasar share fage ta zuwa gasar kur’ani a kasar Iran daga Ghana sun samu kyautar kwafin kur’ani.

Bayanin ya ce makaranta da mahardat biyar ne suka samu nasarar shiga cikin wadanda za su halarci gasar ta kasar daga kasar Ghana bayan da suka samu nasara a gasar share fage da aka gudanar a birnin Akra fadar mulkin kasar.

Wadanda suka samu wannan nasar kuwa su ne Abbas Abubakar Siddiq, Said Isa, Hashim Dawud, Malama Zakiyya Muhammad sani, Yahuza Muhammad kabir, Nurul Haq Yahuza.

Gasar kur’ani ta kasar Iran dai na daga cikin manyan gasar da ake gudanarwa ta duniya da ke samun halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya, inda a wannan karon za a gudanar da gasar a karo na talatin da hudu.

Yanzu haka dai cibiyar da ke kula da harkokin shirya gasar kur’ani ta kasa ta bayyana cewa, ta kammala dukkanin shirinta na gudanar da wannan gasa, kuma tuni aka aike da goron gayyata zuwa sauran kasashe.

3591094


captcha