IQNA

An Bude wata Babbar Cibiyar Kur’ani A Libya

23:53 - April 19, 2017
Lambar Labari: 3481420
Bangaren kasa da kasa, an bude wata babbar cibiyar hardar kur’ani mai tsarki a birnin Aujla na kasar Libya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alwasat cewa, an bude wannan cibiya ne tare da halartar manyan mutane da suka hada da dattijan kabilun larabawa na yankin da kuma malamai gami da jami’ai.

Babbar manufar bude wannan cibiya dai ita ce karfafa ayyuka da suka shafi kur’ani a wanann yanki mai tsohon tarihi a kasar Libya.

Ma’aikatar kula da ahrkokin addini ta kasar Libya ita ce ta dauki nauyin bude wannan cibiya, wadda jama a yankin suke bayyana cewa za ta taima matuka ga ‘ya’yansu wajen koyar da su kur’ani.

Koyar da hardar kur’ani dai ita ce babbar manufar ciyar da nufin samar da matasa mahardata kur’ani mai tsarki, baya ga haka kuma za a kara da wasu abubuwan na daban, kamar koyar da tajwidi da sauransu.

3591084


captcha