IQNA

Matashi Ba’iraniye Ya Samar Da Hanyar Tattaunawa Tsakanin Addinai A Amurka

23:55 - April 19, 2017
Lambar Labari: 3481421
Bangaren kasa da kasa, wani yaro matashi dan asalin kasar Iran ya samar da watahanya ta tattaunawa a tsakanin addinai a jahar Colarado ta kasar Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kjct8 cewa, Emad Shahnushi wani matshi ne dana salin kasar Iran ya kirkiro da wata hanya wadda za ta bayar da dama ga mabiya addinai su hadu a kan fahimtar juna.

Wannan matashi ya kira taro na farko wanda ya hada da manyan jami’an yan sanda na jahar Colarado da kuma wasu daga cikin masana na musulmi.

Babbar manufarsa kamar yadda ya sheda ita ce samar da fahimtar juna atsakanin dukkanin mabiya addinai da kuma musulmi, musamman yadda ake ci gaba da samun matsaloli na rashin fahimta musamman a kan musulmi.

Ya ce wannan shi ne dalilin da yasa ya kira shirin nata da taken ka fahimci makwabcinka musulmi, domin ta hanyar jin ta bakin kowa alokacin ne za ka fahimci mutum da akidarsa da kuma manufarsa.

Daga karshe dai mahalarta wannan taro da ia kira sun nuna gamsuwa matuka da irin wannan tunani da yaro matashi da ke bai kammala makarantar sakandare ba yake da shi, wanda suke ganin kuma yin hakan zai taimaka matuka.

3591134

captcha