IQNA

IQNA Na Watsa Gasar Kur’ani Kai Tsaye A Kan Instgram

23:31 - April 21, 2017
Lambar Labari: 3481425
Bangaren zamantakewa, kamfanin dillancin labaran kur’ani na kasa da kasa na watsa gasar kur’ani ta duniya da ke gudana a birnin Tehran kai tsaye a manhajar instgram.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, tun daga ranar farko da aka fara gudanar da gasar kur’ani mai tsarki ta duniya, yana watsa gasar kur’ani ta duniya da ke gudana a birnin Tehran kai tsaye a manhajar instgram.

Bayanin ya ce Iqna yana watsa wannan gasa a dukkanin bangarorin gasar, da suka hada da gasar ta bai daya kamar yadda aka saba, sai kuma bangaren gasar kur’ani ta mata, bayan kuma a bangaren gasar kur’ani ta duniya wadda ta kebanci nakasassu.

Ga masu bukatar bin wannan gasa kai tsaye domin ganin yadda take gudana, za su iya shiga cikin manhajar instgram na kamfanin dillancin labaran kur’ani na kasa da kasa wato IQNA ta wannan hanya: @iqnanews daga nan har zuwa karshen gasar.

3591231


captcha