IQNA

Mahardacin Kur'ani Dan Kenya:

Na Hardace Kur'ani A Cikin watanni 8 / Ina Fatan Zuwa Na Daya

23:29 - April 22, 2017
Lambar Labari: 3481428
Bangaren kasa da kasa, wani maharadcin kur'ani mai tsarki dan kasar Kenya ya bayyana cewa ya hardace kur'ani a cikin watanni takwas.

Haisam Safar Ahamd dan shekaru 26 da haihuwa dan kasar Kenya ya bayyana cewa, ya hardace kur'ani mai tsarki tun yana dan shekaru 10 da haihuwa, kuma hardar ta dauke shi tsawon watanni takwas ne kawai.

Wannan makaranci kuma mahardaci ya bayyana cewa, a lokacin da ya kudiri aniyar hardace kur'ani mai tsarki, ya ajiye dukkanin abubuwa na wasanni na kuruciya, inda ya mayar da hankali kaco kaf a kan hardar kurani.

Ya ce ya samu nasara ne wajen cimma burinsa na hardace wannan littafi mai tsarki, tare da taimakon Allah, da kuma karfin gwiwar da mahaifansa suka ba shi, inda a kowane lokaci suke nuna masa cewa zai iya hardace kur'ani.

Yanzu haka dai wannan matashi mahardacin kur'ani na daga cikin wadanda suke wakiltar kasar Kenya a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta duniya da ake gudanarwa yanzu haka a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran.

Tun daga lokacin da aka fara gasar, wannan matashi dan kasar Kenya ya yi ta samun nasara tun aga mataki nafarko har zuwa yanzu, ida yanzu haka yana daga cikin wadanda suka tsallake zuwa mataki na karshe na gasar.

Wanann gasar dai ana gudanar da ita ne tare da halartar makaranta da mahardata daga kasashen duniya tamanin da uku, kuma za a kwashe mako guda ana gudanar da gasar.

3591898
captcha