Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin almisriyun cewa, cibiyar kula da harkokin Palastinawa da ke gidan Kason Isra'ila ta bayyana cewa jami'an Isra'ila suna kwace kur'anai daga hannun Palastinawa da suke tsare da su.
Bayanin ya ci gaba da cewa yana daga cikin matakan masu tsaren gidajen Kason suke dauka a cikin kwanakin nan da nufin takura ma Palastinawan, wanda hakan ya yi hannun riga da dukkanin kaidoji da dokoki na kasa da kasa.
Cibiyar ta ce tana kira ga dukkanin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa da su sa baki a cikin wannan lamari na cin zarfin bil adama da ake yi a cikin gidajen Kason Isra'ila.
Yanzu haka dai wasu daga cikin fursunonin palastinawa da Isa'ila take tsare da su sun shiga yajin cin abinci domin nuna rashin amincewa da yadda ake yin mu'amala da su tamkar ba 'yan adam ba a gida Kason haramtacciyar kasar Isra'ila.
3591872