IQNA

Ana Gudanar da Tarukan Shahadar Imam Musa Kazim (AS)

23:40 - April 22, 2017
Lambar Labari: 3481430
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da tarukan tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Musa Kazim (AS) a birnin Kazimai tare da halartar mutane fiye d miliyan daya da dubu 900.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labaran Saumaria News cewa, tun daga ranar Laraba da ta gabata ce dubun-dubutar mutane daga koina cikin Iraki da ma wasu kasashe suke ci gaba da isa birnin Kazimain.

Wannan dai na daga cikin tarukan da Mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah ke gudanarwa na tunawa da shahadar limamin ahlul bait Imam Musa Kazim (AS).

Mahukuntan kasar ta Iraki sun ce ya zuwa yau dai mutane kimanin miliyan daya ne da dubu 900 suka isa hubbaren Imam Kazim  S da ke garin na Kazimain a arewacin birnin Bagadaza na kasar Iraki

Ana su bangaren jami'an tsaro sun dauki dukkanin matakan tsaro domin tabbatar da cewa an gudanar da wannan taruka lafiya, musamman bayan kame wasu 'yan ta'addan wahabiyawa da suke shirin kai harin bama-bamai a wurin tarukan.

3592089
captcha