IQNA

Taron Tunawa Da Shahadar Imam Kazim (AS) A Tanzania

23:21 - April 23, 2017
Lambar Labari: 3481431
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron tunawa da shahadar Imam Musa Kazim (AS) a yankuna daban-daban na kasar Tanzania.

Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Tanzania ya sanar da cewa, mabiya ahlul bait (AS) a fadin kasar sun gudanar da tarukan tunawa da shahadar Imam Kazim a(AS).

Bayanin ya ce wadannan taruka da suka gudana a birane na kasar Tanzania, na daga cikin irin tarukan da mabiya tafarkin ahlyl bait (AS) suke gudanarwa a kowace sheakara, domin samun albarcin wadannan bayin Allah.

Daya daga cikin malaman mazhabar ahlul bait a kasar Sayyid Nur Alridha ya gabatar da jawabi a kan matsayin Imam Musa Kazim (AS) da kuma tarihin rayuwarsa, gami da darussan da suke kunshe a cikin rayuwarsa mai albarka.

Baya ga haka kuma ayau an gudanar da wani taron a cibiyar Abbas (AS) wanda ya kebanci mata zalla, domin tunawa da shahadar Imam Kazim (AS) wada kuma cibiyar tana a birnin Darussalam ne na kasar ta Tanzania.

3592667






captcha