IQNA

Paparoma A Masar:

Dole Ne Addinai Su Tattauna Kan Yaki Da Tsatsauran Ra'ayi

23:38 - April 30, 2017
Lambar Labari: 3481451
Bangaren kasa da kasa, a ziyarar aikin da Paparoma Francis shugaban darikar katolika ta mabiya addinin kirista ta duniya ke gudanarwa a kasar Masar ya gana da shugaban kasar Abdul-Fatah Al-Sisi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta alalam ta habrat cewa, a ganawar da ta gudana tsakanin Paparoma Francis da shugaban Masar Abdul-Fatah Al-Sisi a yau Asabar: Paparoma Francis shugaban darikar katolika ta mabiya addinin kirista ta duniya ya jaddada wajabcin daukan matakan kalubalantar akidar wuce gona da iri a matsayin wani yanki na yaki da ta'addanci.

Har ila yau Paparoma Francis ya bayyana cewa; Tashe-tashen hankula da matakan wuce gona da iri suna da alaka da kwadayin mulki, neman kudi ta hanyar fataucin muggan makamai da kuma akidar tsaurin ra'ayin addini.

A nashi bangaren shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ya bayyana cewa kawo karshen ayyukan ta'addanci yana bukatar hadin gwiwa da taimakekkeniya tsakanin kasashen da suke makobtaka da ma sauran kasashen duniya baki daya.

A yau Asabar ne ake sa-ran fara gudanar da zaman tattaunawa tsakanin Paparoma Francis shugaban darikar katolika ta mabiya addinin kirista ta duniya da Ahmad Tayyib shugaban jami'ar Azhar na kasar Masar kan hanyoyin wanzarda zaman lafiya da sulhu tsakanin mabiya addinin Musulunci da na kirista.

3594524

captcha