IQNA

Kyautata Harkokin Karatun Kur'ani A Kasar Iretria / Makarantun Allo

21:53 - May 17, 2017
Lambar Labari: 3481522
Bangaren kasa da kasa, ana shirin kyautata makarantun kur'ani da ake gudanar da karatun allo a kasar Iretria wadanda su ne asali ta fuskar karatu kur'ani a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kasar Iretria tana daya daga cikin kasashen Afirka adda ta fice daga kasar Habasha a shekara ta 1993, tare da zama kasa mai cin gishin kanta.

Kasar ta Iretria dai wadda ke gabashin Afirka tana da mutane fiye da miliyan 6 kuma fiye da kashi sattin da biyu daga cikinsu mabiya addinin kirista ne.

Kasantuwar musulmin kasar addinin muslucni ya zo musu ne daga kasashen arewacin Afirka, sun dauki hanyoyi da ake amfani da su wajen koyar da karatun addini a kasashen arewacin nahiyar Afirka, musamman ta fuskar karatun kur'ani da kuma harda, inda ake yin amfani da allon itace wajen yin karatu.

Daga cikin hanyoyin da ake amfani da su ta wannan hanya, ana rubuta ayoyin kur'ani mai tsarki mataki bayan mataki, dalibi yana karantawa yana maimaitawa har sai ya goge sosai akan abin da yake karantawa kafin ya cirata zuwa ayoyi ko surori na gaba.

Malaman da suke koyar da karatun kur'ani mai tsarki a kasar bisa ga al'ada sukan kasance mahardata ne, a kan haka sukan dora dalibai a kan tafarkin harda idan suna da sha'awa, amma mafi yawncin lokuta daliban sukan fara ne da karatu kafin kaiwa mataki harda.

Akwai matakin sauka, wanda ke nufin kammala karatun kur'ani baki daya daya ta hanyar rubuta shi aya bayan aya akan allon itace, wanda kuma hakan yana baiwa dalibi damar rike abin da ya karanta, saboda yana nanata shi da yawa.

A halin yanzu cibiyoyin musulmi a kasan suna son bullo da wani sabon salon inganta irijn wadannan makarantu na allo a kasar, tare da samar musu da hanyoyi na zamani wajen karatun, ba tare da sun bar salonsu na asali ba wato karatun kur'ani a kan allo.

Da dama daga cikin malaman irin wadannan makarantu dai sun yi na'am da wannan mataki, inda suka bayyana shirinsu na amincewa da hakan, domin kara habbaka harkar kur'ani mai tsarki a kasar.

Musulmi a kasar Iretria suna zaune lafiya tare da mabiya addinin kirista ba tare da wata matsala ba, inda dukaknin su suke girmama juna, kamar yadda kuma sukan halarci tarukan juna, da nufin karfafa yanayin zamantakewa ta zaman lafiya a tsakaninsu.

3600250


captcha