IQNA

Zaman Taro Kan Harkokin Mulki A Cikin Kasashen Musulmi A Tunisia

21:59 - May 17, 2017
Lambar Labari: 3481524
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro a kasar Tunisia a kan sh'anin mulki a cikin kasashen musulmi da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ina cewa, cibiyar yada ilimi da aladun muslunci ta duniya ISESCO ita ce ta dauki nauyin shirya wannan zaman taro, tare da hadin gwiwa da bangaren yaki da cin hanci da rashawa da yada al'adun muslunci na ma'aikatar al'adu ta kasar Tunisia.

Daga cikin muhimamn abubuwan da taron zai mayar da hankali a kansu akwai batun yadda ya kamata a kara bayar da dama ga jama'a fararen hula su shiga a dama da su a cikin harkokin mulkin kasashensu, maimakon mayar da su saniyar ware, kamar yadda hakan shi ne yake gudana a mafi yawan kasashen larabawa.

Kamar yadda kuma taron zai kara karfafa gwiwar mahukunta akan yadda za su yaki ayyukan cin hanci da rashawa a cikin kasashensu, musamman ma dai kasashen ad suke da tsari na dimukradiyya daga cikin kasashen na musulmi.

Taron zai samu halartar jami'ai da masana a kan harkokin mulki da al'adu da kuma tattalin arziki daga kasashen Jordan, Iraki, Yemen, Palastine, Masar, Tunisia, Aljeriya, Morocco, Saudiyya, Libya, da kuma Malaysia.

3600616


captcha