Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na ikhlas ya bayar da rahoton cewa, Aiden Oinar ‘yar wani kauce a yankin Dujerh a cikin kasar Turkiya.
Ta bayar da labarin cewa ta rayu ba tare da ta iya karaun kr’ani ba, amma bayan da tsofa ya kamata, ta yi nadama kan hakan, inda ta rika zuwa makaranta tare da yara tana zama tana sauraren karatun da ake koyar da su.
Ta kara da cewa a cikin ikon Allaha cikin sheakara guda da ta fara halartar ajujuwan koyar da karatun kur’ani, sai gas hi ta fara iyawa, ama daga bisani harshenta yak are tana karanta kur’ani a duk kuwa da cewa shekarunta sun haura tamanin.
Daga karshe ta ce tana yin nasiha da kuma kira ga matasa da yara mas karncin shekaru musulmi, da su mike su yi amfani da lokacinsu wajen koyon addini da kuma karatun kur’ani mai tsarki, tun kafin damar da suke da ita ta kubuce musu.
Kamar yadda kuma ta yi godiya ga Allah madaukakin sarki a kan ni’imar da yay yi mata tare da bata damar koyon kur’ani tana cikin shekarun tsufa.