IQNA

Tattaunawa Tsakanin Mata Mabiya Addinai A AmurkaDomin Sanin Muslunci

19:59 - May 18, 2017
Lambar Labari: 3481527
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman tattaunawa atsakanin mata mabiya addinai domin samun masaniya akan addinin musluncia jahar Florida ta Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labara na wfit cewa, an gudanar da wannan zaman taro wanda kungiyoyin mata musulmi suka gayyata, da nufin kara samun fahimtar juna da zaman lafiya atsakanin mabiya sauran addinai da musulmi.

A yayin gudanar da zaman, an samu halartar mata daga addinan kiristanci da kuma yahudanci gami da sauran mata musulmi, inda suka tattauna a kan muhimman abubuwa da suke da muhimmanci a fahimta akan addinin muslunci da kuma zamantakewar musulmi da sauran addinai.

Matan musulmi sun bayyana wa sauran mata mabiya addinai cewa musulunci baya da matsala da wani addini, yana zama lafiya da kowa, domin kuwa babu tilasci a cikin addini wannan shi ne abin da kur’ani ya sheda wa msuulmi, saboda haka suna tare da kowa kuma suna girmama mahangar mutane.

Kamar yadda kuma suka tabbatar da muhimamncin zaman lafiya da fahimtar juna da kaunar juna atsakanin musulmi da sauran dukkanin mabiya addinai.

Aana samun karuwar kyamar msuulmi a halin yanzu a cikin kasashen turai sakamakon bayyanar kungiyoyin ‘yan ta’adda masu kasha jama’a da sunan jihadi, kamar yadda kuma aka samu bullar kungiyoyi masu fakewa da hakan domin nuna kyama ga msuulmi.

3600700


captcha