IQNA

Wani Masani Daga Lebanon Kan Zaben Iran

20:04 - May 19, 2017
Lambar Labari: 3481530
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Shams masani kuma mai sharhi daga kasar Lebanon kan harkokin Iran, ya bayyana mahangarsa dangane da zaben da ake gudanarwa a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin radio nur na kasar Lebanon cewa, Muhammad Shams malamin jami'a kuma mai sharhi kan harkokin Iran ya bayyana cewa, zaben da ake gunarwa a Iran ya nuni da tasirin da tsarin muslunci ya yi a kasar ne

Ya ci gaba da cewa, babban abin fahimta daga yadda ake gudanar da zabe a kasar Iran shi ne, kasar tana bin tsarin addinin muslunci a siyasance da kuma sauran harkoki na gudanarwa da kuma zamantakewa amma bisa zabin jama'a.

Masanin ya yi ishara da cewa, babu wani wanda aka tlastawa cewa dole ne ya fito ya yi zabe ko kuma ga wanda zai zaba acikin 'yan takara, ana yin zaben bisa 'yanci da kuma gamsuwar mutum da dan takarar da yafi kwanta masa.

Muhammad Shams ya ce; ko da jagoran juyin juya halin kasar ana zabarsa, ne, ba mukami ne na har abada ba, domin kuwa ana gudanar da zabe na mambobin majalisar kwararru, wadanda su kuma su ne suke gudanar da zaben jagora, idan wa'adinsa yak are za su iya sabunta masa wani wa'adin ko kuma su zabi wani, kamar yadda suke da hakkin su cire shi idan ya saba wa kaidoji da dokoki na jamhuriyar muslunci.

Jin ra'ayin jama'a ya nuna cewa kimanin kashi 70 cikin dari na mutanen da suka cancanci kada kuri'a ne za su fito zaben.

3600917


captcha