IQNA

Taron Kammala Horo A Kan Rubuce-Rubucen Musulunci

23:27 - May 20, 2017
Lambar Labari: 3481532
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen wani taro da aka gudanar a kasar Uganda a kan muhimman abubuwan da aka rubta a tarihin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga bangaren yada labarai na cibiyar yada al’adun muslunci cewa, an gudanar da taron ne tare da halartar shugaban ifishin yada al’adun muslunci na Iran a kasar Uganda Ali Bakhtiyari, da kuma Sheikh Sulaiman Gusule babban mai bayar da fatawa na kasar da kuma mataimakinsa.

Haka nan kuma taron ya samu halartar masana da malamai daban-daban da suka hada da sheikh Yusuf Mulunba shugaban cibiyar kula da ayyukan kur’ani da iyalan gidan manzo na kasar.

A wurin taron bababn malami mai bayar da fatawa na kasar ya gabatar da jawabi, inda ya jinjina wa jamhuriyar musulunci ta Iran dangane da kokarin da take wajen karfafa ayyukan da suka shafi hada kan al’ummar msuulmi da dunke barakar da ke tsakaninsu.

Horon ya dauki tsawon kwanaki ana gabatar da shi, inda wadanda suka samu horon suka kaddamar da abubuwan da suka rubuta akai, daga karshe kuma aka zabi wadanda suka fi nuna kwazo, wadanda suka samu kyautuka a wajen taron kammala horon.

Ofishin raya al’adun muslunci na Iran da ke kasar Uganda ne dai ya dauki nauyin wannan horo, tare da bayar da dukkanin abubuwan da ake bukata domin gudanar da shi da kuma daukar nauyin dukkanin wadanda suka halarci daga sassa na kasar ta Uganda.

3601322


captcha