IQNA

Cibiyar Musulmin Amurka Kan Jawabin Trump

Saboda Da Kyautata Alaka Da Kasashen Musulmi Ba Dalili Ba Ne Na Kare Masu Kama Karya

23:01 - May 22, 2017
Lambar Labari: 3481539
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar musulmin Amurka ta mayar da martani dangane da kalaman Donald Trump a gaban taron da Saudiyya ta kira a birnin Riyadh.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin PRNewsWire ya bayar da rahoton cewa, babbar cibiyar musulmin Amurka ta nuna rashin gamsuwa da jawaban da Trump ya gabatar a taron da Saudiyya ta kira.

Cibiyar ta ce Trump ya kauda kansa daga irin maganganun da yake yi wadanda suka doru a kan akidarsa na kymar musulmi, inda ya nuna cewa tamkar shi yana son hada kai da kasashen musulmi, domin yaki da ‘yan ta’adda masu kai hare-haren ta’addanci da sunan addinin muslunci.

A lokacin da yake yake gabatar da jawabin nasa, Trump ya kauda kansa daga batun masu daukar nauyin ayyukan ta’addanci da yake magana a gabansu, wadanda suke da hannun harin sha daya ga watan satumbanmanyan ‘yan kama karya da ke mulki a kan al’ummar saudiyya.

Cibiyar wadda ta hada manyan lauyoyi muslmi na Amurka, ta yi Allawadai da yadda Trump da sarakunan kama karya na larabawa suka yi wasa da hankulan jama’a da suka tara dama sauran al’ummomin duniya, kan cewa ‘yan ta’addan da suke kai hare-haren ta’addanci da suna jihadi a kasashen duniya cewa Iran ce ke daukar nauyinsu, alhali Saudiyya a fili take fadi kan cewa ita ce ke daukar nauyin ‘yan ta’addan wahabiyya a Iraki da Syria da sauransu.

3601952


captcha