IQNA

‘Yan Sanda Sun Ki Amincewa Da Kisan Musulma A Matsayin Ta’addanci

23:48 - June 20, 2017
Lambar Labari: 3481627
Bangaren kasa da kasa, ‘yan sandan Amurka a jahar Virginia sun ki amincewa da kisan da aka yi wa wata budurwa musulma a matsayin aikin ta’addanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Guardian ta bayar da rahoton cewa, bayan kisan da aka yi wa budurwa musulma mai suna Nabra Hassanen ‘yar shekaru 17 a garin Reston na jahar Virginia a Amurka, ‘yan sanda ajahar sun musunta cewa aikin yana da alaka da kyamar musulmi.

Babban jami’in ‘yan sanda na jahar Virginia Jolly Parker ya bayyana cewa, bisa binciken da suka gudanar sun gane cewa lamarin ya faru ne sakamakon wata rigima tsakanin wasu matasa, inda wani matashi ya fito daga mota yana dukar wasu ‘yan mata da suka hada har Nabra, amma bayan wasu sa’oi an tsinci gawarta kilo mita biyar daga wurin da abin ya faru, amma lamarin bai da alaka da ta’addanci ko kyamar addini.

Shedun gani da ido sun ce Nabra tare da kawayenta sun kammala sallar magariba ne a masalaci, sun tsaya wani wurin cin abinci suna buda baki tare da kawayenta a lokacin da matashin ya kawo musu hari kuma ya sace Nabra, daga bisa aka tsinci gawarta bayan ya kashe ta, lamarin da mahaifanta suka danganta da kyamar musulmi da ake yi a kasar ta Amurka, wanda yake karuwa bayan hawan Donald Trump kan kujerar mulkin kasar.

3611460


captcha