IQNA

A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Musulmi Ne Kawai Ke Da Matsala

23:50 - June 20, 2017
Lambar Labari: 3481628
Bangaren kasa da kasa, a sansanonin da musulmi ‘yan gudun hijira suke ne a kasar Afirka ta tsakiya ake samun matsalar rashin abinci.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalti daga shafin Aljazeera cewa, Maja'miar garin Bangaso ta sanar da cewa musulmi 1500 da su ke zaman gudun hijira a cikinta, suna fuskantar karancin abinci.

Maja'miar garin Bangaso ta sanar da cewa musulmi 1500 da su ke zaman gudun hijira a cikinta, suna fuskantar karancin abinci.

Tashar telbijin din al-jazeera ta bada labarin cewa barkewar wani sabon rikicin a tsakanin kungiyoyin musulmi da kiristoci ya jawo kwararar dubban 'yan gudun hijira.

'Yan kungiyar "Anti Balaka' ta mabiya addinin kirista sun kai hari a masallacin garin "Bangaso" inda su ka kashe limami da masu salla.

'Yan gudun hijirar musulmi da su ke cikin cocin garin na Bangaso,suna fuskantar karancin abinci saboda yadda kungiyar ta "Anti Balaka" ta hana akai musu agaji.

Kakakin dakarun tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya velademir Mantiro, ya ce; Babu aminci akan hanyar cocin idan ace musulmin za su so fitowa.

Musulmi ne dai suka fi fuskantar matsala daga ‘yan kungiyar ‘yan daba ta kiristoci da suke yi musu kisan kiyashi da yankan rago saboda dalilai na banbancin addini, duk kuwa da cewa sauran musulmi da kiristoci a kasar suna zaune lami lafiya a tsakaninsu kafin wannan rikici.

3610738


A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Musulmi Ne Kawai Ke Da Matsala

A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Musulmi Ne Kawai Ke Da Matsala

A Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira Musulmi Ne Kawai Ke Da Matsala

captcha