IQNA

Za A Gudanar Da taron ranar Quds A Kenya

23:57 - June 21, 2017
Lambar Labari: 3481631
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron ranar Quds ta duniya a kasar Kenya a ranar Juma'a mai zuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, bangaren yada labarai na cibiya yada ala'dun musulunci ya habarta cewa, a ranar Juma'a mai zuwa kasar Kenya na daga cikin kasashen da za a gudanar da taron ranar Quds.

Bayanin y ace bisa la'akari da yadda yanayin al'ummar kasar yake da kuma karbuwar da wannan rana take da shia a wajen musulmi, ya zama ala tilas a gudanar da taro wanda zai hada bangarori.

Daga karshe bayanin y ace wannan yana daga cikin gajiyar juyin juya halin muslunci na Iran wanda ya ginu a kan kare manufofin al'ummar musulmi da muslunci ba tare da nuna wani banbanci a tsakanin musulmi ba.

3611244


captcha